3 Yuli 2015 - 13:18
Amurka ta nemi a dage zaben Burundi

Kasar Amurka ta roki kasar Burundi da ta jinkirta gudanar da zaben shugaban kasar da ake shirin yi 15 ga wannan wata na Yuli, inda shugaba mai ci Pierre Nkurunziza ke neman wa’adin shugabanci na uku.

John Kirby mai Magana da yawun ma’aikatar waje ya roki shugaban Burundi Pierre Nkurunziza da ya nemi warware rikicin kasar ta hanyar tattaunawa da ‘yan adawa maimakon yin yadda ya so.

Jimillan mutane 70 suka mutu a rikicin kasar da aka shafe watanni biyu ana zanga-zangar adawa da Pierre Nkurunziza.

Masu da ido dai na Majalisar Dinkin Duniya sun soki zaben ‘Yan Majalisu da aka gudanar a ranar Litinin.

Amurka na son a dage zaben shugaban kasa har sai an mahukunatan kasar sun samar da hurumin da za a gudanar da karbabben zabe.

A ranar Litinin ne dai kasashen gabashin Afrika za su gana a Tanzania domin tattauna yadda za a shawo kan rikicin kasar Burundi.288